(ABNA24.com) Rundunar sojojin sama na kasar Iran ta fara wani gagarumin atisai a tsakiyar kasar wanda ta bashi suna “Shiryatarwan Jagora ta 98”.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar ya nakalto kwamandan sojojin sama na kasar Iran Burgediya Janar Alireza Sabahi-Fard yana cewa atisayin wanda aka fara shi a safiyar yau Alhamis zai yi amfani da yanki mai tazarar kilomita murabba’I 416,000 a cikin lardin Semnan.
Sabahi-Fard ya kara da cewa sojojin sama na kasar zasu gwada sabbin makamai da kayakin aiki na yaki sabbi da suka samu a wannan atisayen.
Har’ila yau sojojin zasu gwada yadda zasu kare kasar daga duk wani yakin da zai taso a yankin tekun Farisa da mashigar ruwa ta Hurmuz.
Gwamnatin kasar Iran dai ta sami gagarumin ci gaba a bangaren kera makamai da kuma kayakin aiki na kare sararin samaniyar kasar wadanda suka hada da na’urorin Rada da kuma makamai masu linzami daban-daban.
Banda haka sojojin kasar suna gudanar da atisayin sojojin kasar akai-akai don shirin ko ta kwana.
/129